Saturday 31 January 2026 - 00:19
Kariyar Malaman Iraƙi ga Wilayar Ayatullahil Uzma Khamenei; Jamhuriyar Musulunci ita ce "Katangar Ƙarshe" kuma Jagoranta "Hussainin Zamani Ne"

Hauza/Yayin mayar da martani ga makircin maƙiya, ƙungiyar malaman Najaf ta fitar da wata sanarwa, inda ta bayyana Jamhuriyar Musulunci a matsayin "katangar ƙarshe", ta kuma jaddada goyon bayanta ga shugabancin Ayatullah Khamenei, ta kuma siffanta shi da "Hussainin zamani".

A cewar rahoton rukunin fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, a lokacin kololuwar fada tsakanin gaskiya da ƙarya, inda maƙiyan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke yunƙurin fuskantar ta da kowane irin shaidanun makirce-makirce, "Ƙungiyar Malaman Najaf" ta fitar da wata sanarwa, inda ta sake jaddada alkawarinta ga wannan tsarin mai tsarki a ƙarƙashin shugabancin hikima na Ayatullah Khamenei.

Fassarar Sanarwar:

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.

(Kuma haƙiƙa Mun rubuta a cikin Zabura bayan Ambato (Alƙur'ani) cewa, zan gadar da ƙasata ga bayina salihai) (Anbiya' – 105).

A wannan lokaci na tarihi, lokacin da yaƙi tsakanin rundunar gaskiya da rundunar mulkin mallaka na duniya ya tsananta, kuma abokan gaba suka sanya mu tsakanin zaɓi biyu: "Fafatawa da Kaskanci", ƙungiyar malaman Najaf tare da taken 'Haihata minaz zilla' tana sake jaddada alkawarinta ga "Katanga ta Ƙarshe", tushen izza da karamci, wato Jamhuriyar Musulunci ta Iran; tsarin da ya ta'allaka ne akan "Wilayatul Faqih" kuma ana gudanar da shi a ƙarƙashin shugabancin hikima na Ayatullah Khamenei (rayukanmu su zama fansarsa). A cikin wannan ƙungiyar tamu, mun ɗauki goyon bayanmu ga "Wilayatul Faqih" ba a matsayin wani matakin siyasa na wucin gadi kawai ba, sai dai a matsayin alkawari na shari'a wanda ya samo asali daga imani. Domin wannan hukuma ita ce mafakar Shi'awa da Musulmi, kamar yadda aka ambata a cikin hadisi mai daraja: "Ƙasar Qom, mazauni ne ga 'yayan gidan Annabi Muhammad (SAWA) kuma mafakar Shi'armu." Kuma yazo cewa ita ce tafarkin samar da tashin motsin shugabanmu, Mai zamanin (Ajfs).

Duk wani hari ga Jamhuriyar Musulunci – ta hanyar yaƙin ruwan sanyi ko matsin lamba na tattalin arziki – yana nufin kai hari ga ginshiƙin bukkar kuma haɗari ga dukan masu 'yanci a duniya, kuma mun ɗauki rayuwar mu da asali da mutuncinmu a cikin ci gaba da wanzuwarta. Saboda haka, dukan abubuwan da muke da su na zahiri da na ma'ana, zamu yi amfani da su a ƙarƙashin tutar shugabanta wanda shi ne "Hussainin Zamani", (don kare shi).

Har ila yau, muna taya al'ummar Iran da kwamandojin wannan ƙasa murnar tsayin daka mai ban mamaki; wani tsayin daka wanda kowace rana ke tabbatar da cewa "Falalar Allah" ce ke gudanar da fagen fama, kuma yana nuna cewa niyyar masu rauni a ƙarshe za ta ci nasara. Saboda haka, muna gayyatar daukacin jama'ar ƙasarmu da su kasance farkakku kuma masu wayo, kuma su guji "gubar kafofin watsa labarai" wanda makasudin su shine yanke alaƙa da cibiyar wilaya. Kuma muna jaddada cewa basira ita ce kada mu zama kibiya a cikin bakar maƙiyan Allah da za a harba zuwa jijiyar wilaya.

Iran za ta ci gaba da girma, kuma Waliyul Faqih zai kasance fitilar da zata haska mana hanya lokacin duhun fitina. Matsin lamba ba za su haifar da kome ba face ƙarin ƙarfin riƙon "Igiyar Allah mai ƙarfi".

(Lalle Allah yake kare waɗanda suka yi imani).

Ƙungiyar Malamai ta Najaf

10 ga Janairu, 2024(M) – 20 ga Rajab, 1447(HQ), 20 ga Dey, 1404(HS)

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha